Kada wani Daya yayi Hukunci tsakanin Mutum biyu a halin yana Fushi

Kada wani Daya yayi Hukunci tsakanin Mutum biyu a halin yana Fushi

An karbo daga Abdurrahman Dan Abi Bakrata yace:"Babana ya rubuta-ko na rubuta masa-izuwa Dansa Ubaidullah Dan Abi Bakrata shi yana Alkali a Sajistan:Kada kayi Hukunci tsakanin Mutum Biyu kana mai-fushi,domin cewa naji Manzan Allah-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-yana cewa:kada Daya yayi Hukunci tsakanin Mutum biyu yana mai-fushi".Acikin wata ruwayar:"Kada Mai-Hukunci ya yanke Hukunci tsakanin Mutum Biyu alhali yana mai-fushi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Mai-Shari'a Mai-Hikima ya hana Mai-Hukunci yayi Hukunci tsakanin Mutum Biyu alhali yana Mai-Fushi:Domin cewa Fushi yana tasiri abisa Ma'aunin Mutuntakar Mutum saboda haka ba'a amince ya zalunci ko ya kuskurewa gaskiya ba cikin Halin Fushinsa:sai hakan ya kasance zalunci abisa wanda Hukuncin ya hau kansa kuma Tabewa ga wanda yayi Hukunci da Zunubi akansa.

التصنيفات

Ladaban Alqali