Mai tsira da amincin Allah ya hana yin salla bayan Asuba har sai rana ta hudo, haka nan bayan 'La'asar har sai ta fadi

Mai tsira da amincin Allah ya hana yin salla bayan Asuba har sai rana ta hudo, haka nan bayan 'La'asar har sai ta fadi

Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da shi- yace: wasu yardaddun mutane sun bada sheda a waje na -a guri na wanda yafi kowa a cikinsu shi ne Umar- cewa Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- ya hana yin sallar nafila marar dalili bayan Asuba har sai rana ta fito,da kuma bayan La'asar har sai rana ta fadi" Daga Abu Sa'id-Allah ya yarda da shi- daga -Manzo tsira da aminci su tabbbata a gare shi- ya ce:"ba'a yin sallar nafila bayan Asuba har sai rana ta hudo, hakanan bayan La'asar har sai ta fadi

[Ingantacce ne] [Buhari da Muslim suka rawaito shi da ruwayoyin sa]

الشرح

Annabi -tsira da amincin Allah- ya hana yin salla bayan Asuba har sai rana ta fito ta daga gwargwadon tsawon mashi yadda ido zai iya ganinta,gwargwadon minti biyar zuwa sha biyar,gwargwadon yadda malamai suka yi bayani.Haka nan yayi hani ga salla bayan La'asar har sai rana ta fadi,gabanin sallar Magariba da 'yan mintintina,,saboda yayi kamanceceniya da mushirikai wanda ke bautaw rana lokacin fitowar ta ko faduwarta,kuma an hana yin kamanceceniya dasu wajen ibada,har yace duk wanda yayi kama da wasu jama'a to yana cikinsu.

التصنيفات

Lokutan da aka hana yin Sallah