a yayin da wani mutum ke tsaye a filin arfa, kwatsam sai ya fado daga kan dabbar da yake kai, sai ta taka shi- ko kuma ya ce: ta kayar da shi sai manzon Allah ya mai tsira da aminchi ya ce: ku wankeshi da ruwa da kuma magarya, ku yimasa likkafani a cikin tufafin sa, kada ku saka masa turare ko…

a yayin da wani mutum ke tsaye a filin arfa, kwatsam sai ya fado daga kan dabbar da yake kai, sai ta taka shi- ko kuma ya ce: ta kayar da shi sai manzon Allah ya mai tsira da aminchi ya ce: ku wankeshi da ruwa da kuma magarya, ku yimasa likkafani a cikin tufafin sa, kada ku saka masa turare ko kafur, kada ku lullube masa kan shi, domin shi za`a tashe shi a ranar alqiyama yana talbiyyah

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

a yayin da wani mutum daga cikin sahabbai ke tsaye a filin arfa akan dabbar sa a lokacin Hajjin ban kwana yana cikin kayan ihrami sai ya fado daga kanta, sai wuyan sa ya karye ya mutu, sai manzon Allah mai tsira da aminchi ya umurce su da suyi masa wanka kamar yadda akewa sauran mamata yan`uwansa, da ruwa, da magarya su yimasa likkafani a cikin kwarjallen sa da mayafin sa, wadanda ya daura harama da su tare da cewa yayi harama da Hajji da kuma alamu na aikin ibada da suke tare da shi, hakika manzon Allah mai tsira da aminchi ya hana su da su saka masa turare ko su rufe kan sa ya ambata musu hikimar da ke cikin yin haka, ita ce Allah zai tashe shi akan abinda ya mutu akai, shi ne yin talbiyya, wadda ita ce alamar mutum yana cikin aikin hajji

التصنيفات

Abubuwan da aka hana a Ihrami