An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai haila

An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai haila

Daga Abdullahi Dan Abbas -Allah ya yarda da su- yace: "An umarci mutane dasu yi dawafi ga dakin Allah a karshe,sai dai anyi sauki ga mace mai haila".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Dakin Ka'aba yana da daraja da daukaka,kuma shi wata alama ce ta bautar Allah da kankan da kai da tsoron Allah,kuma yana da kwarjini a zukatan mutane,rayuka sun damfaru da shi,suna son shi.Don haka Annabi ya umarci mahajjaci daya sanya dawafi ga dakin Allah abu na karshe,ya zama ban kwana,sai dai anyi sauki ga mace mai haila don gudun kar ta bata masallacin.wannan kuma ya shafi Hajji ne kawai banda Umra.Duba littafin Taisiril Allam,Tanbihul Afham,Ta'asisil Ahkam.

التصنيفات

Falalar musulunci da kyawawan koyarwarsa, Sifar yanda ake Aikin Hajji