Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi-yana numfashi wajen shan ruwa sau uku

Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi-yana numfashi wajen shan ruwa sau uku

Daga Anas Dan Malik - Allah ya yarda da shi - ya ce:"Manzon Allah -tsira da aminci su tabbata a gare shi-yana numfashi wajen shan ruwa sau uku"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance yana sha, yana numfashi a cikin abin sha sau uku, yana sha, sa'annan ya raba kwano da bakinsa, sannan ya sha na biyu, ya raba kwanon da bakinsa, sannan ya sha na uku, kuma ba ya numfashi a cikin kwanon.

التصنيفات

Abincinsa SAW