Mun fito tare da Manon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin watan Azumin Ramalan, cikin wani matsanancin zafin rana, har sai da takai dayanmu yana dora hannunsa akan sa sabida tsananin zafin Rana kuma cikinmu babu mai Azumi sai Manzon Allah in Tsira da Amincin Allah su tabbata…

Mun fito tare da Manon Allah Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi a cikin watan Azumin Ramalan, cikin wani matsanancin zafin rana, har sai da takai dayanmu yana dora hannunsa akan sa sabida tsananin zafin Rana kuma cikinmu babu mai Azumi sai Manzon Allah in Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi da kuma Abdullahi Dan Rawaha

Daga Abu Addarda'i -Allah ya yarda da shi- Mun fito tare da Manon Allah -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi- a cikin watan Azumin Ramalan, cikin wani matsanancin zafin rana, har sai da takai dayanmu yana dora hannunsa akan sa sabida tsananin zafin Rana kuma cikinmu babu mai Azumi sai Manzon Allah in Tsira da Amincin \Allah su tabbata a gare shi-da kuma Abdullahi Dan Rawaha

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Abu Al-dardaa yana bada labari _ Allah yarda da shi- cewa sun futo a lokacin wata tafiya a cikin watan Ramalana, kuma ranar ta kasance mai tsananin zafi ce, har ya kai cewa sabida tsananin afinta dayan su yana dora hannunsa a kansa don ya kare rana mai tsanani, kuma duka cikinsu babu Mai Azumi sai Annabi -Tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi , da kuma Abdullahi Dan Rawaha Al-ansari - Allah ya yarda da shi hakika su biyun sun jure tsananin kuma sunyi Azumin wanda wannan yana nuna halascin yin Aumi a tafiya duk da wahalar da take ciki wacce batakai matsayin wacce zata kai hallaka ba .Taisir Al-allam (shafi27) Tabih Al-afham (Mujalladi 3/432) Ta'asisu Al-ahkam3/241).

التصنيفات

Azumin Masu Uzuri