Babu wata ciyarwarsa agareki

Babu wata ciyarwarsa agareki

Daga fadima yar Kaisu -Allah ya yarda da su- "cewa lallai Abu Amr Dan Hafs ya sake ta saki uku kuma gashi baya nan (acikin wata riwaya: "Ya sake ta saki uku" to sai ya aika wakilinsa da Acca, sai ta ji haushinsa, sai ya ce: kuma Wallahi baki da hakkin komai a kanmu sai tazo wajen Annabi ta gaya masa yadda akai, sai ya e da ita Baki da wata ciyarwa akansa (kuma acikin wani lafazi: "kuma babu wurin zama" sai Annabi ya Umarce ta cewa da tayi Idda a Dakin Ummu sharik; sannan ya ce: Waccan Mata ce da Sahabbaina suna yawan zuwa wurinta; kiyi Idda a gidan Ibn Ummu Maktoom doncewa shi Makaho kina iya ajiye kayanki, kuma idan kin gama idda to ki Sanar da ni, sai ta ce: bayan na gama na sanar da shi cewa Mu'awiya Dan abu Sufyan da kuma Abu Jahamsun zo neman Aure na, sai Annabi ya ce: Amma Abu Jaham to akwashi da dukan Mata, kuma amma Mu'awiya to Talaka ne bashi da kudi, ki Auri Usama Dan Zaid, sai taji bata sonsa, sannan ya ce mata ki Auri Usama Dan zaid sai ta Aure shi sai Allah ya sanya Alkahiri a cikin Auren, kuma tayi ta Alfahari da shi".

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Abu Amr Dan Hafs ya nisanta daga Matarsa ta hanyar saki Matarsa Fadima Yar Kais, kuma wannan shi ne karshen Saki ne a gare ta, kuma duk wacce aka saka saki uku batada ciyarwa akan Mijinta, sai dai shi ya aika mata da Acca, sai ta zaci cewa ciyar da ita Wajibi ne akansa Matukar dai tana cikin Idda, sai ta raina Acca din kuma taji bata so,sai ya rantse cewa batada komai akansa, sai ta kai kararsa zuwa ga Annabi, sai ya bata labari cewa batada komai akansa kuma bata da wurin zama, kuma sai aka Umarce ta cewa tayi Idda a cikin gidan Ummu Shuraik, kuma yayin da aka gayawa Annabi cewa Ummu Shuraik Sahabbai Maza suna yawan zuwa gidanta, sai ya Umarce ta tayi Idda a gidan Dan Maktoom kasancewarsa Makaho ne, kuma bazai ganta ba koda ta cire kayanta kuma ya ce ta gaya masa idan ta gama Idda. Yayin da ta gama Idda sai Mua'wiya ya nemi Aurenta, da kuma Abu Jahm, sai ta nemi shawarar Annabi a cikin haka. sabida cewa Nasiha wajibi ce -Musamman ga wanda aka nemi shawararsa- to cewa bai mata shawara ba da ko daya; sabida Abu Jahm akwai shi da Tsanani ga Mata kuma shi Mu'awiya talaka ne bashi da kudi, kuma sai ya Umarce ta da ta Auri Usama, sai taji bata sonsa kasancewar sa Bararren Bawa ne, kuma sai dai ita tabi Umarnin Annabi, sai ta karbe shi, kuma tayi farin ciki da hakan, kuma Allah ya sanya Alkairi mai yawa a ciki.

التصنيفات

Hukunce Hukunce da Mas'alolin Saki