Ba'a hada tsakanin Mace da gwaggwanta ko kuma tsakaninta da Innar ta

Ba'a hada tsakanin Mace da gwaggwanta ko kuma tsakaninta da Innar ta

Daga Abu Huraira -Allah ya yarda sa shi- zuwa ga Annabi : "Ba'a hada tsakanin Mace da gwaggwanta ko kuma tsakaninta da Innar ta"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Wannan Shari'a Mai tsarki ta zo da dukkan abinda yake Alkairi ce cikinsa da kuma gyara Al'umma kuma ta yaki dukkan abinda yake akwai cuta a cikinsa ko kuma barna, daga cikinsu cewa ta kwadaitar akan hadin kai da kuma soyayya da kauna, kuma ta hana kyama da kuma yake hulda da kuma gaba, to sabida hartawar da Sharia tayi wa yawaita Mata wanda hakan wasu Maslahohi suka janyo shi, kuma Mafi yawan tara mata ga Namiji, yana jawo gaba da kuma kiyayya a tsakaninsu, sabida abinda ya ke faruwa na kishi, sai Annabi ya hana cewa to hakan kada ya kasance tsakanin Yar'uwa da Yar'uwa ko kuma a aurar da Gwaggon mace akan 'Yar Dan'uwanta, ko kuma Yar ya akan Innarta, da Sauransu, kuma daga ciki koda za'a kadara cewa daya daga cikinsu Namiji ko kuma Mace, to ya haramta ya aureta sabida dangantaka sabida cewa bai halarta a hada su ba kuma anan in akayi sun hadu, kuma wannan Hadisin yana kebance wani gamewa na fadin Allah Madaukaki inda yake cewa: {Kuma an halasta muku auren wadan da ba wadan nan ba}

التصنيفات

Waxanda aka haramta a Aura