"Wani Mutum Muslmi bai taba zama a Masallaci ba don Sallah da Zikiri, Sai Allah yayi farin ciki da shi, Kamar yadda Iyalin Matafiyi suke yi idan ya dawo Musu"

"Wani Mutum Muslmi bai taba zama a Masallaci ba don Sallah da Zikiri, Sai Allah yayi farin ciki da shi, Kamar yadda Iyalin Matafiyi suke yi idan ya dawo Musu"

An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- daga Annabi -tsira da Amincin Allah a gare shi- ya ce: "Wani Mutum Muslmi bai taba zama a Masallaci ba don Sallah da Zikiri, Sai Allah yayi farin ciki da shi, Kamar yadda Iyalin Matafiyi suke yi idan ya dawo Musu"

[Hasan ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Musulmn da ya Lazamci zuwa Masallatai don yin Sallah da yin Zikiri a cikin su kuma ya dawwama kan hakan, to Allah Madakaki yana farin ciki da shi, kamar yadda Iyalan Matfiyi suke yi idan ya dawo, kuma bai halatta a fassara kalmar Murna ba da Rahama ko Tausayi ko waninsu, aa ya wajaba a tabbatar da su Sifar Allah Madaukaki ce ba tare da Juyawa ba ko canzawa ko korewa kuma ba tare da kwatantawa ba ko Kamantawa, wannan kuma tare da Sanin cewa Murna tana hade da Tausayi da jin kai, Allah shi ne Mafi Sani.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi