Sayyadin Abubakar -Allah ya yarda da shi- ya shiga wajen wata Mata daga Kabilar Ahmas ana kiranta da Zainab, sai ya ganta bata Magana

Sayyadin Abubakar -Allah ya yarda da shi- ya shiga wajen wata Mata daga Kabilar Ahmas ana kiranta da Zainab, sai ya ganta bata Magana

An rawaito daga Kais Bn Abi Hazim, ya ce: Sayyadin Abubakar -Allah ya yarda da shi- ya shiga wajen wata Mata daga Kabilar Ahmas ana kiranta da Zainab, sai ya ganta bata Magana? Sa suka ce: tayi rantsuwar Hajji ne ba tare da Magana ba, sai ya ce da ita: kiyi maganarki, cewa hakan bai halatta ba, wannan yana daga cikin aikin Jahiliyya, sai tayi Maganarta.

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Abubakar -Allah ya yarda da shi ya shiga wajen wata Mata a cikin Kabilar Ahmas sunan ta Zainab, sai ya sameta bata magana, sai ya tambayeta mai yasa bata magana sai suka ce: tayo Hajji ne bata Magana, sai ya ce da ita: kiyi maganarki, saboda barin maganar baki daya bai halatta ba; saboda cewa shi ya Kasance daga cikin Ibadun Jahiliyya sannan sai Musulunci ya Haramta shi, kuma shigar Namiji zuwa mace ba tare da zargi ba ko kadaita kamar yadda Sayyadina Abubakar yayi -Allah ya yarda da shi- ya halatta.

التصنيفات

Rantsuwa da kuma Bakance