Duk wanda ya bini to hakika yabi Allah, kuma duk wanda ya Sabamun to hakika ya sabawa Allah, kuma duk wanda yabi Sugabansa to hakika ya bini, kuma duk wanda ya Sabawa Shugaba to hakika ya sabamun

Duk wanda ya bini to hakika yabi Allah, kuma duk wanda ya Sabamun to hakika ya sabawa Allah, kuma duk wanda yabi Sugabansa to hakika ya bini, kuma duk wanda ya Sabawa Shugaba to hakika ya sabamun

An rawaito daga Abu Huraira -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya bini to hakika yabi Allah, kuma duk wanda ya Sabamun to hakika ya sabawa Allah, kuma duk wanda yabi Sugabansa to hakika ya bini, kuma duk wanda ya Sabawa Shugaba to hakika ya sabamun"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi SAW yayi bayanin cewa biyayya gare shi tana daga cikin biyayya ga Allah, kuma Annabi SAW baya Umarni sai da Shari'a wacce Allah ya Shar'anta ga Al'ummarsa to idan yai Umarni da da wani abu to shi Sharia ne kuma duk wanda ya bi shi to ya bi Allah, kuma duk wanda ya saba Masa to ya sabawa Allah, kuma Shugaba idan Mutum ya bi shi to hakika ya bi Manzo SAW kuma idan ya Saba masa to hakika ya sabawa Manzon; domin Annabi SAW shi wanda ya yi umarni da hakan a cikin mafi yawan Hadisai; sai dai in yayi Umarni da Sabo

التصنيفات

Haqqin Shugaba kan Talakawa