Lallai cewa Abdullahi bn Abi Aufa yayi Kabarbaru Hudu a jana'izar 'ya mace, don haka sai ya tashi bayan ta hudu abunda yake tsakanin Kabbarorin biyu yana neman gafararta sai ya yi addu'a, sannan ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh - ya kasance yana yin hakan

Lallai cewa Abdullahi bn Abi Aufa yayi Kabarbaru Hudu a jana'izar 'ya mace, don haka sai ya tashi bayan ta hudu abunda yake tsakanin Kabbarorin biyu yana neman gafararta sai ya yi addu'a, sannan ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh - ya kasance yana yin hakan

Daga Abdullah bn Abi, yardar Allah ta tabbata a gare su, ya ce: "Lallai cewa Abdullahi bn Abi Aufa yayi Kabarbaru Hudu a jana'izar 'ya mace, don haka sai ya tashi bayan ta hudu abunda yake tsakanin Kabbarorin biyu yana neman gafararta sai ya yi addu'a, sannan ya ce: Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare sh - ya kasance yana yin hakan": Kuma a wata ruwaya: Ya yi kabbara sau Hudu , sai ya zauna wani lokaci har sai da nayi zaton zai yi kabbara ta biyar ne, sannan ya yi sallama a damansa da hagu. Lokacin da ya tafi, sai muka ce masa: Menene wannan? Ya ce: Ba zan kara muku ba a kan abin da na ga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya aikata, ko kuma: Wannan shi ne yadda Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi

[Hasan ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Hakim Ya Rawaito shi]

الشرح

Abdullahi bn Abi Aufa - Allah ya yarda da shi - ya ba da labarin cewa ya yi Sallar jana’izar ‘yarsa, don haka sai ya yi Mata Kabbara hudu, kuma bayan ta hudan yayi Mata Addu'a Kuma ya nema mata gafara da dalla-dalla game kan hakan. shine ya yi kabbara ta shiga salla, sannan ya karanta fatiha, sannan ya ce a ta biyun kuma, sai ya yi salati ga Annabi mai tsira da amincin Allah, sannan ya yi kabbara ta uku, sannan yayi wa mamacin Addu'a, sannan ya Kabbara ta Hudu. Kuma Abdullahi bn Abi Aufa - Allah ya yarda da shi - ya ce bayan ya yi sallama ga wadanda suka yi salla tare da shi: Haka Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi. Wato yayi Kabbara Hudu kuma yayi Addu'a ga Mamaci bayan ta huɗu. Kuma a cikin wata ruwaya: Ya cewa shi yayi Kabarbari hudu, sa’an nan ya yi Masa Addua kuma ya nemi gafara bayan ta huɗun, har sai ya tabbatar da cewa a bayansa za a ce ta biyar kuma, sannan ya gabatar da Sallama biyu: ta farko a gefen dama, kuma ta biyu a na hagu, kamar sallah .Kuma bayan cikar Sallar wani da yake bayansa ya tambayeshi Dangane da dalilin jinkirinsa bayan kabbarar ta huxu, kuma bai Sallama daga ia ba nan ba, sai ya ce: Abin da kuka yi ba shi da wani abu da ya wuce abin da Manzon Allah - SAW. An ruwaito ijma'i a kan haka, kamar yadda yake a cikin Al-Mughni na Ibnu Qudamah, kuma wannan hadisin ya kasance hadisi Hasan ne a wajen Al-Albani, amma akwai Sabani a tsakanin malamai dangane da ingancin sa. Domin a cikin isnadinsa akwai Ibrahim Al-Hijri, wanda yake mai rauni ne, kuma akwai Hadisin marfoo'i da ya zo a cikin Sallama daya, kuma a cikinsa akwai Irsali.

التصنيفات

Yadda ake sallah ga Mamaci