Idan xayanku zai yi sallah to ya stuce sallarsa, ko da da Kibiya ne

Idan xayanku zai yi sallah to ya stuce sallarsa, ko da da Kibiya ne

Daga Samra Bn Ma'abad Al-Juhani -Allah ya yarda da shi- daga Manzon Allah SAW ya ce: "Idan xayanku zai yi sallah to ya stuce sallarsa, ko da da Kibiya ne"

[Ingantacce ne] [Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Wannan Hadisin yana bayanin Mustahabbanci ga Mai sallah ya sanya Sutura a gabansa, kuma lallai cewa Suturar tana iya yiwuwa da komai da mai Sallah zai kafa shi a gabansa, koda kuwa gajere ne kamar kibiya, kuma a cikin wannan akwai Alamu na sauqin Shari'a da rangwamenta

التصنيفات

Sunnonin Sallah