Manzon Allah ya yi tsayuwar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani

Manzon Allah ya yi tsayuwar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani

Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace "Manzon Allah ya yi tsayuwar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani"

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Wannan Hadisin yana nuna cewa Manzon Allah SAW yayi Sallah a cikin Dare Sallar dare da Aya xaya daga cikin Qur'ani yana ta Maimaitata bai karanta komai ba sai ita, kuma a fili ita ce wannan Ayar da take cewa: "In kayi musu Azaba to su Bayinka ne kuma idan ka gafarta musu to kaine Mabuwayi kuma mai hikima" [Ma'ida: 118] kamar yadda yazo a wasu riwayoyin Hadisin

التصنيفات

Tsayuwar Dare