Idan Allah ya so karvar ran wani Bawansa a wata Qasa sai ya sanya wata buqata a can

Idan Allah ya so karvar ran wani Bawansa a wata Qasa sai ya sanya wata buqata a can

An karvo daga Abi Izza Al-huzali -Allah ya yarda da shi- ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Idan Allah ya so karvar ran wani Bawansa a wata Qasa sai ya sanya wata buqata a can"

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Idan Allah yayi nufin Mutuwar Bawa daga cikin Bayinsa a Wata Qasa ta Musamman baya cikin ta, sai Allah ya sanya masa Buqata a wannan Qasar, kuma idan ya tafi buqatar tasa a wannan Qasa sai Allah ya karvi ransa, da kuma abunda Allah ya Qaddara kuma ya rubuta Masa babu makawa sai ya faru gare shi kamar yadda ya Qaddara shi, kuma wannan yana daga cikin Imani da Hukuncin Allah da Qaddara

التصنيفات

Mas’alolin Hukuncin Allah da Kaddara Musulunci