Cewa wata Baiwa an same ta an mata rotse akanta a tsakanin Duwatsu biyu

Cewa wata Baiwa an same ta an mata rotse akanta a tsakanin Duwatsu biyu

An rawaito daga Anas Bn Malik –Allah ya yarda das hi- ya ce: “Cwa wata baiwa an sameta an rotse mata kai a tsakanin Duwatsu biyu, sai aka ce waye yai miki wannan ? wane da wane ne? har aka fadi wani Bayahude, sai ta tayi nunin E da kanta, Sai Annabi SAW ya yi Umarci da a rotse kansa a tsakanin Duwatsu guda biyu” kuma a wata riwayar Muslim da Nasa’i: “Cewa wani Bayahude ya kasha wata Baiwa ta Hanyar roste kanta, sai Manzon Allah ya daukar mata Haddin”

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

An samu wata baiwa a lokacin Manzon Allah SAW an rotse mata kai a tsakanin duwatsu biyu, nbata karasa Mutuwa, sai suka tambayeta ta hanyar kirga mata sunaye wadanda ake sa ran sunyi mata abun, har suka zo kan sunan wani Bayahude sai ta yi nuni dakanta cewa E, wannan shi ne wanda ya rotse mata kan, sai ya zamanto abun tuhuma da kasha ta, sai suka kama shi suka titsiye shi har yayi Ikirarin da Kashe ta, saboda wani adon Azurfa a jikinta, Sai Annabi SAW yayi Umarni a saka masa da kwatankwacin, sai aka roste kansa shi ma a tsakanin duwatsu biyu.

التصنيفات

Qisasi