Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalha

Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida, da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalha

Daga Abdullah Dan Umar -Allah ya yarda dasu- zuwa ga Annabi: Manzo tsira da amincin Allah sun shiga gida,da Usama Dan Zaidu da Bilal da Usman Dan Dalha sai aka rufe musu kofar, bayan an bude: sai na zama farkon wanda ya shiga, na gamu da Bilal, sai na tambaye shi: shin Manzo tsira da aminci ya yi salla? sai yace e,ya yi tsakanin ginshikai guda biyu

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Lokacin da Allah madaukaki ya bude makha, ya tsarkake dakinsa daga gumaka da butunbutumai da hotuna, sai tsira da aminci ya shiga Dakin Ka'abaa madaukakiya, a tare da shi akwai mai yi masa hidima, Bilal da Usama,da mai kula da gida Usman Dan Dalha,sai aka kulle musu kofa don kada mutane su yi cincirindo wajen shigowar Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi,don su ga ydda yake yin bauta, gudun kar su shagaltar da shi daga abin da yake son yi a wajen,shi ne ganawa da Ubangijinsa tare da gode masa bisa ni'imominsa, yayin da suka jima suna jira , sai aka bude kofar.Abdullahi Dan Umar ya kasance mai tsananin kwadayin bibiyar Sunnar Annabi ne don haka ya zama farkon wanda ya shiga bayan an bude kofar.Sai ya tambayi Bilal : shin Annabi ya yi salla anan ciki ne? sai Boilal yace: e, ya yi salla a tsakanin ginshikan can na bangaren dama .a lokacin Ka'aba Mai tsarki tana da ginshikai shida ne,sai ya sanya uku a bayansa,biyu a damansa daya kuma a hagunsa, kuma ya bar tazara kamu uku tsakaninsa da katanga, sai sallaci raka'a biyu, kuma ya yi addu'a abangarori hudu.

التصنيفات

Saraxan Sallah