An zuwarwa Manzon Allah SAW da wani Mutum ya Sha Giya, sai ya ce: "Ku masa Duka"

An zuwarwa Manzon Allah SAW da wani Mutum ya Sha Giya, sai ya ce: "Ku masa Duka"

Daga Abu huraira -Allah ya yarda da shi- ya ce: An zuwarwa Manzon Allah SAW da wani Mutum ya Sha Giya, sai ya ce: "Ku masa Duka" sai Abu huraira ya ke cewa: daga cikin mu akwai mai dukansa da hannu da Mai dukansa da Takalmi, da mai dukansa da tufarsa, yayin da ya juya sai wasu daga cikin Mutane suka ce: Allah ya Qasqantaka, sai ya ce: "Kada ku ce haka, kada ku taimakawa shixan a kansa"

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

التصنيفات

Haddin Shan Giya