Wani Malami daga Malaman Yahudawa yazo wajan Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai yace:Ya Muhammad,hakika mun samu cewa Allah zai sanya Sammai akan yatsa,kuma kassai akan Yatsa,kuma Bishiyu akan Yatsa,kuma Ruwa akan Yatsa,kuma Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halittu akan…

Wani Malami daga Malaman Yahudawa yazo wajan Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai yace:Ya Muhammad,hakika mun samu cewa Allah zai sanya Sammai akan yatsa,kuma kassai akan Yatsa,kuma Bishiyu akan Yatsa,kuma Ruwa akan Yatsa,kuma Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halittu akan Yatsa,sannan yace:Nine Mamallaki.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan.Sannan ya karanta:"Kuma basu kaddara Allah Hakikanin ikonsa ba, kuma Kasa duka damkarsa ce a Ranar Kiyama"?.Acikin wata Ruwaya ta Muslim:"Da Duwatsu da Bishiyu akan Yatsa,sannan ya girgizasu sannan yace:Nine Mamallaki,nine Allah".Kuma acikin wata Ruwaya ta Buhari:"Zai sanya Sammai akan Yatsa,kuma Ruwa da Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halitta akan Yatsa"

An karbo daga Dan Mas'ud Allah ya yarda dashi yace:"Wani Malami daga Malaman Yahudawa yazo wajan Manzon Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi sai yace:Ya Muhammad,hakika mun samu cewa Allah zai sanya Sammai akan yatsa,kuma kassai akan Yatsa,kuma Bishiyu akan Yatsa,kuma Ruwa akan Yatsa,kuma Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halittu akan Yatsa,sannan yace:Nine Mamallaki.Sai Annabi tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan.Sannan ya karanta:Kuma basu kaddara Allah akan Hakikanin ikon yinsa ba kuma Kasa duka damkarsace a Ranar Kiyama?.Acikin wata Riwaya ta Muslim:"Da Duwatsu da Bishiyu akan Yatsa,sannan ya girgizasu sannan yace:Nine Mamallaki,nine Allah".Kuma acikin wata Riwaya ta Bukhari:"Zai sanya Sammai akan Yatsa,kuma Ruwa da Kasa akan Yatsa,kuma sauran Halitta akan Yatsa"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Dan Mas'ud-Allah ya yarda dashi-yana bamu labari cewa wani Mutum daga Malaman Yahudawa yazo wajan Annabi-tsira da amincin Allah su tabbata agareshi-ya ambata masa cewa sun samu cikin Littattafansu cewa Allah -tsarkakekken Sarki-Ranar Al-kiyama zai sanya Sammai a Yatsa,kuma kassai a Yatsa,kuma Bishiyu a Yatsa,kuma Kasa aYatsa,.Awata Riwayar:kuma Ruwa akan Yatsa,kuma sauran ababan Halitta akan Yatsa,dagaYatsunsa-Mai-Girma da Daukaka-,kuma ita Biyarce kamar yadda yazo acikin Riwayoyi ingantattu,kuma ba kamar Yatsun ababan Halitta bace,kuma cewa shi zai bayyana wani abu daga Ikonsa da Girmansa Mai-Girma da Daukaka sannan sai ya girgizasu kuma ya bayyana Mulkinsa na Hakika,da cikar tasarrufinsa saki ba kaidi da Uluhiyyarsa ta Gaskiya.Sai Manzan Allah tsira da amincin Allah su tabbata agareshi yayi Dariya har Fikokinsa suka bayyana saboda gasgata fadin Malamin Yahudawan,sannan ya karanta:{Kuma basu kaddara Allah akan Hakikanin ikon yinsa ba Kasa duka damkarsa ce a Ranar Kiyama}.

التصنيفات

Tauhidin Sunaye da Siffofi