Manzon Allah tsira da amincin Allah ya kasance yana sallar Asuba, Muminai mata suna zuwa lullube da mayafansu, sannan su koma gidajensu ba wanda ke gane su, saboda sauran duhun dare.

Manzon Allah tsira da amincin Allah ya kasance yana sallar Asuba, Muminai mata suna zuwa lullube da mayafansu, sannan su koma gidajensu ba wanda ke gane su, saboda sauran duhun dare.

Daga Aisha -Allah ya yarda da ita- tace: (Manzon Allah tsira da amincin Allah ya kasance yana sallar Asuba, Muminai mata suna zuwa lullube da mayafansu, sannan su koma gidajensu ba wanda ke gane su, saboda sauran duhun dare

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Aisha -Allah ya yarda da ita tana ambata mana cewa: Matan Sahabbai sun kasance suna lullube jikinsu da tufafinsu kuma su je sallar Asuba tare da Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, kuma har su koma gidajensu ba mai gane su, duk da kasancewar haske ya dan fara bayyana, tare da sauran duhun. Littafin Taisiril Ahkam, na Malam Bassam, shafi na 86

التصنيفات

Saraxan Sallah