Idan ina da kwatankwacin zinare, da na yi farin ciki da cewa darare uku ba za su wuce ni ba alhali ina da wani abu daga ciki sai wani abu da nake bi bash

Idan ina da kwatankwacin zinare, da na yi farin ciki da cewa darare uku ba za su wuce ni ba alhali ina da wani abu daga ciki sai wani abu da nake bi bash

Daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - wanda ya ce: "Idan ina da kwatankwacin zinare, da na yi farin ciki da cewa darare uku ba za su wuce ni ba alhali ina da wani abu daga ciki sai wani abu da nake bi bashi."

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim Suka Rawaito shi amma lafazin na Bukhari ne]

الشرح

Idan da a ce ina da kudin adadin Dutsen Uhud na zinare tsantsa, da na kashe su duka saboda Allah, ban bar komai ba sai abin da nake bukata domin biyan hakkoki da biyan bashin da ke kaina.

التصنيفات

Zuhudu da tsantseni, Zargin Son Duniya