Lallai cewa wani Mutum ya tambayi Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da Azumi a lokacin tafiya sai ya ce: "idan kaga dama kayi Azumi in kuma kaga dama ka sha ruwanka"

Lallai cewa wani Mutum ya tambayi Annabi tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi game da Azumi a lokacin tafiya sai ya ce: "idan kaga dama kayi Azumi in kuma kaga dama ka sha ruwanka"

Daga Nana Aisha -Allah ya yarda da ita- Cewa Hamza Dan Amr Al'aslami ya ce da Annabi: Shin zan iya yin Azumi a lokacin tafiya? kuma ya kasance Mai yawan Azumi, sai yace: Idan kaga dama kayi Idan kuma kaga dama kada kayi

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Nana Aisha Allah ya yarda da ita cewa Hamza Dan Amr Al'aslami ta bada labarin Annabi cewa shi yana yin Azumi a tafiya? sai Annabi ya bashi zabin yin Azumi ko kin yinsa sai ya ce: "idan ka ga dama kayi Azumi Kuma idan kaga Dama kada kayi" kuma abinda yake nufi da Azumin a nan shi ne Azumin Farilla; Sabida fadin Annabi: "wannan Sauki ne daga Allah" kuma wannan ya nuna cewa shi ya tambaya ne game da Azumin farilla, kuma yana nuna cewa abin da Abu Daud ya rawaito, in ya ce: "Ya Manzon Allah lallai ni Ma'abocin wani abin Hawa ne inaTafiya a kansa kuma ina bada hayarsa, kuma ni cewa wani lokaci watan azumi yana riskata a halin in jin karfin jikina" Har zuwa karshen Hadisin, kuma daga wannan ne yake nuna cewa shan ruwa a tafiya sauki ne daga Allah kuma duk wanda yai ruko da ita to ya dace, kuma duk wanda yayi Azumi yayi Azuminsa, kuma hakan ya nuna ya sauke wajibinsa. Taisir Al'allam(Shafi na 325) Tanbih alafham (3/429) Ta'asis Al'ahkam, (3237).

التصنيفات

Falalar Sahabbai -Allah yayarda da su-, Abunda ya Halatta ga Masu Azumi