A kowane dare Annabi yana wutiri ko a farkon dare ko tsakiyarsa, ko karshensa, Kuma yakan tsaida Wutirinsa da Asuba

A kowane dare Annabi yana wutiri ko a farkon dare ko tsakiyarsa, ko karshensa, Kuma yakan tsaida Wutirinsa da Asuba

Daga Nana Aisha ya ce: "A kowane dare Annabi yana wutiri ko afarkon dare ko tsakiyarsa, ko karshensa, Kuma yakan tsaida Wutirinsa da Asuba"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Nana Aisha tana bada labari game da lokacin da Annabi ya kasance yake sallatar Wuturi a cikin Dare, kuma cewa bai takaita a wani lokaci daya ba a kowane lokaci na dare yana yin Wuturi, wani lokacin ma a farkonsa lokacin da zai Sallaci Isha da kuma ya sawwaka bayant, kuma wani lokacin a tsakiyar daren bayan wucewar daya bisa ukunsa na farko, wani lokacin kuma daga karshensa lokacin da biyu bisa ukunsa suka shude, har ya kasance karshen lokacin Dare.

التصنيفات

Tsayuwar Dare