Annabi ya kasance yana Karantawa a Sallar Asubar Ranar Jumua : Suratu Sajada, kuma Suratul Insan

Annabi ya kasance yana Karantawa a Sallar Asubar Ranar Jumua : Suratu Sajada, kuma Suratul Insan

Daga Abu Huraira ya ce: "Annabi ya kasance yana Karantawa a Sallar Asubar Ranar Jumua : Suratu Sajada, kuma Suratul Insan"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Ya kasance a Al'adar Annabi cewa yana karanta a Sallar Asuba ranar Jumua, suratu sajada cikakkiya, kuma wannan a raka'ar farko bayan Fatiha, kuma yana karantawa a Raka'a ta biyu bayan Fatiha Suratu al'insan; don wa'azantarwa da abinda wadan nan Surorin na abubuwan da zasu faru Masu girma da kumawadan da suka faru a wannan Rana, Kamar halittar Annabi Adam, da kuma Tunasarwa da Ranar Alkiyama da kuma tashi da Wasunsunsu

التصنيفات

Koyarwarsa SAW a Sallah