Manzon Allah -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kasance- yana yin huduba guda biyu alhali yana tsaye, yana raba tsakanin su da zama.

Manzon Allah -tsira da amincin Allah su kara tabbata a gare shi ya kasance- yana yin huduba guda biyu alhali yana tsaye, yana raba tsakanin su da zama.

An karbo daga Abdullahi dan umar dan khaddabi- Allah ya kara yarda a gare su su biyun- ya ce: { Annabi tsira da aminci su kara tabbata a gareshi ya kasance yana yin hudubobi guda biyu yana zama a tsakanin su } a wata ruwayar ta jabir- Allah ya kara masa yarda-: { manzon Allah tsira da amincin Allah su kara tabbata a gareshi- ya kasance yana yin hudubobi guda biyu alhali yana tsaye, yana raba tsakanin su da zama }.

[Ingantacce ne duka Riwayoyin nasa guda biyun] [Al-Baihaki ne Ya Rawaito shi]

الشرح

Ranar juma`a matattara ce babba gamammiya ga mutanen gari baki dayan su saboda haka ne annabi tsira da aminci sukara tabbata a gareshi ya kasance daga cikin hikimar sa yana yiwa mutane huduba ranar juma`a hudubobi guda biyu, yana fuskantar da su izuwa dukkan alherai a cikin hudubobin guda biyu, yana tsawatar da su ga barin sharri ya kasance yana zuwa da hudubobi guda biyu alhali yana tsaye akan munbari, don ya kasance ya kai isa matuka cikin koyar da su da yimusu wa`azi, da abinda ke ciki na tsayuwa wajen bayyanar da karfin musulunci da bashi cikakkiyar kulawa. idan ya gama da hudubar farko, sai ya zauna zama sassauka don ya dan huta, sai ya raba tsakanin ta farko da ta biyu, sa`annan ya mike yayi huduba ta biyu saboda kada mai huduba ya gaji mai sauraro kuma ya kosa.

التصنيفات

Sallar Jumu'a