"Lallai wata Mata ta zo Wajen Manzon -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da Wata Riga da aka saka"

"Lallai wata Mata ta zo Wajen Manzon -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- da Wata Riga da aka saka"

A kan Sahl bin Saad - yardar Allah ta tabbata a gare shi - cewa wata mata ta zo wajan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - tare da alkyabba mai suttura.ta ce nayi ta ne da hannuna sai Manzon ya karveta yana mai bukatarta sai ya futo mana wani lokaci ya daure da ita sai wani Mutum ya ce ka bani ita banga abu mafi kyawunta! ba Ya ce: "To." Don haka Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya zauna a cikin majalisin, sannan ya dawo ya ninke ta sannan ya aika masa da ita, sai mutanen suka ce masa: baka kyauta ba Annabi - SAW- ya sanya ta cikin buqata, sai ka tambaye shi kuma kasan cewa bai hana wanda ya tambaye shi, sai ya ce: Wallahi ban nemi ya bani badon insanya, amma ni natambaye shi ne don ta zama likkafanina na. Sahl ya ce: ita ce Likafaninsa.

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim ne suka rawaito shi Kwatankwacin sa]

التصنيفات

Baiwa da Kyauta, Karamcinsa SAW