Kar ka saye shi, kar ka dawo da sadakar da ka yi, ko da kuwa dirhami daya aka sayar maka, don kuwa mai karbar abin da ya yi kyauta da shi: kamar mai komar da aman da ya yi ne

Kar ka saye shi, kar ka dawo da sadakar da ka yi, ko da kuwa dirhami daya aka sayar maka, don kuwa mai karbar abin da ya yi kyauta da shi: kamar mai komar da aman da ya yi ne

Daga Umar -Allah ya yarda da shi- yace:"Na bayar da wani doki sabo da Allah,sai wanda dokin ke wajensa ya wulakantar da shi,sai naso in sayi dokin,don ina ganin zai sayar da shi da araha,sai na tambayi Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi-?sai yace: kar ka siya,kada ka karbe abin da kayi sadaka da shi,koda kuwa dirhami daya zai sayar maka da shi,don kuwa mai karbar kyautar da yayi,kamar mai yin amai ya lashe ne.".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- ya taimaki wani mutum akan jihadi a tafarkin Allah. sai ya bashi doki ya yi yaki a kansa, sai mutumin sai mutumin ya kasa ciyar da dokin, ba ya kula da shi, ya gajiyar da shu, har ya rame yayi rauni. Sai Umar yayi niyyar sayen dokin don ya san zai yi sauki sabo da ramewa da raunin da ya yi, sai dai bai yi cinikin dokin ba sai da ya shawarci Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi- game da haka,sai Annabi ya hana shi sayen dokin komai araharsa, saboda wannan abu ne da aka bayar don Allah, kar ka damu da shi,sai ya zama kamar ka dawo da wani bangare na abin da ka bayar ne, don ka riga ka bayar, kuma an kankare zunubanka, datti ya fita daga gare ka, bai kamata ya komo gareka ba, wannan shi yasa aka ambaci cinikin da suna kome duk da cewa saye zai yi.

التصنيفات

Baiwa da Kyauta