Yana daga sunna in ya auri budurwa: sai ya yi kwana bakwai a dakinta sannan ya raba kwana, in kuma bazawara ya aura sai yayi kwana uku a wajenta sannan ya raba kwana

Yana daga sunna in ya auri budurwa: sai ya yi kwana bakwai a dakinta sannan ya raba kwana, in kuma bazawara ya aura sai yayi kwana uku a wajenta sannan ya raba kwana

Daga Anas Dan Malik -Allah ya yarda da shi-yace:"Yana daga sunna idan mutum ya auri budurwa ya kwana bakwai a dakinta sannan ya raba kwana.Idan kuma ya auri bazawara ya kwana uku a dakinta sannan ya raba kwana". Abu Kalabata yace:da na so da nace Anas ya daukaka hadisin zuwa ga Annabi tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Yana daga sunna in mutum ya auri budurwa ya kwana a dakinta har tsawon kwana bakwai don ya dauke mata kewa ya kuma saba da ita sannan ya wayar da kanta game da lamarin aure, don kasancewarta bakuwa a harkar aure, sannan kuma sai ya raba kwana. In bazawara ce ya kwana uku a wajenta, saboda karancin bukatarta akan budurwa cikin wadancan lamuran, wannan hukuncin ya zo ne cikin hadisin da ke da hukuncin dagawa zuwa ga Annabi, don kuwa masu rawaito hadisi in suka ce yana daga sunna, to sunnar Annabi suke nufi, ba ta wani ba, Duk hadisin da aka ce zuwa ga Annabi, ko an daukaka shi, to ana nufin an jingina shi zuwa ga Annabi

التصنيفات

kyawawan Halayya tsakanin Ma'aurata