Babu wani Sauran Maraici bayan Balaga, ko kuma hakurin wuni zuwa dare

Babu wani Sauran Maraici bayan Balaga, ko kuma hakurin wuni zuwa dare

An rawaito daga Ali Bn Abi Dali -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Babu wani Sauran Maraici bayan Balaga, ko kuma hakurin wuni zuwa dare"

[Ingantacce ne] [Abu Daud Ya Rawaito shi]

الشرح

Na farko: ba'a daukar Mutumin da ya balaga Maraya Na biyu: Sun kasance a lokacin Jahiliyya suna bautawa Allah -Mai girma da daukaka- da yin shiru, sai ya zauna wuni guda yayi shiru baya Magana har rana ta fadi, sai ya hana Musulmi yin hakan; saboda wannan yana hana yin Tasbihi da kuma Tahlili da Tahmidi da umarni da kyakkyawan aiki da kuma hani da Mummunan aiki, da Karatun Qur'ani da wanin hakan, kuma har walau yana daga cikin aikin Jahiliyya saboda haka aka hana hakan.

التصنيفات

Rantsuwa da kuma Bakance