Annabi ya hada tsakanin Magriba da Isha kuma kowacce daya akwai Iqama, kuma bai yi tasbihi a tsakaninsu sai a karshe daya.

Annabi ya hada tsakanin Magriba da Isha kuma kowacce daya akwai Iqama, kuma bai yi tasbihi a tsakaninsu sai a karshe daya.

Daga Abdullahi Dan Umar Allah ya yarda da su ya ce: "Annabi ya hada tsakanin Magriba da Isha kuma kowacce daya akwai Iqama, kuma bai yi tasbihi a tsakaninsu sai a karshe daya"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Yayin da rana ta fadi a ranar Arfa Annabi ya juyo izuwa Muzdalifa, sai ya sallaci Magriba da isha, Hadawa a karshen lokacin ta biyu, da Ikama ga kowacce, kuma bai sallaci Nafila; sabida tabbatar da ma'anar hadawar, kuma bai ba bayan su ma don ya sami Isashen hutu, don ya shirywa sauran ragowar aikin Hajjinsa

التصنيفات

Sallar Masu Uzuri