Babu Sallah ga duk wanda bashi da Al-wala, kuma babu Al-wala ga duk wanda bai anbaci sunan Allah ba a Al-walar

Babu Sallah ga duk wanda bashi da Al-wala, kuma babu Al-wala ga duk wanda bai anbaci sunan Allah ba a Al-walar

Daga Abu Huraira. ya ce: Manzon Allah SAW: "Babu Sallah ga duk wanda bashi da Al-wala, kuma babu Al-wala ga duk wanda bai anbaci sunan Allah ba a Al-walar"

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Abu Daud Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Abu Hurairah, Allah ya kara yarda a gare shi, yana fada a cikin wannan hadisi a kan manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - cewa ya yi hukunci cewa sallar wanda bai yi alwala ba, ba ta da inganci, kawai kamar yadda ya shar'anta cewa alwala ga mutumin da bai ambaci sunan Allah a kansa ba bai ce: da sunan Allah ba Kafin alwala, hadisi ya shardanta wajabcin sanya suna yayin alwala, kuma duk wanda ya bari da gangan, to alwalar sa ta baci, kuma duk wanda yayi alwala ba tare da sunanta ba ta hanyar mantuwa ko jahiltar hukuncin musulunci, to alwalar sa tana nan.

التصنيفات

Sunnoni da Ladaban Al-wala