Sunnoni da Ladaban Al-wala

Sunnoni da Ladaban Al-wala

10- Na kasance ɗan aiken Banul Muntafiƙi - ko a cikin jama'ar Bunul Muntafiƙi - zuwa wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, ya ce: Lokacin da muka zo wurin Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - bamu same shi agidansa ba, sai muka samu Nana A'isha uwar muminai, ya ce: Sai ta yi umarni a bamu farfesu, sai aka dafa mana, ya ce: Kuma aka zo mana da ƙina' - ƙina: Shi ne farantin da a cikinsa akwai dabino - sannan Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya zo, sai ya ce: «‌Shin kun samu wani abu ne? ko shin an yi umarni akawo muku wani abu ne?» ya ce: Mukace: Eh, ya Manzon Allah, ya ce: Mun kasance tare da Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi -, lokacin da mai kiwo ya kora tumakansa zuwa garke, atare da shi akwai wani 'yar akuya tana kuka, sai ya ce: «‌Kai wane me aka haifa maka?», ya ce: 'Yar akuya, ya ce: «‌To ka yanka mana babbar akuya a madadinta», Sannan ya ce: «‌Kada ka zaci» bai ce: kada ka zaci «‌Mu saboda kaine muka yankata ba, muna da tumakai ɗari, bama so su ƙaru, idan aka haifawa makiyayin 'yar akuya, sai mu yanka babbar akuya a madadinta» Ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai ni ina da wata mata, akwai wani abu a harshenta - yana nufin bata iya magana ba - ya ce: «‌To ka saketa», ya ce: Na ce: Ya Manzon Allah, lallai sahabiya ce, kuma ina da ɗa tare da ita, ya ce: «‌To ka umarceta» Yana cewa ka yi mata wa'azi, «‌Idan akwai alheri a tare da ita zata aikata, kada ka daki matarka kamar yadda kake dukan baiwarka», sai na ce: Ya Manzon Allah ka bani labari game da alwala, ya ce: @«‌Ka cika alwala, ka tsettsefe tsakanin yatsu, ka kai matuƙa a kuskurar baki sai dai idan ka kasance mai azimi ne».