إعدادات العرض
Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi
Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi
Daga Uƙuba ɗan Amir - Allah Ya yarda da shi - ya ce: Mun kasance muna kiwon raƙuma sai zagayena ya zo sai na korosu garke da daddare sai na riski Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - a tsaye yana karantar da mutane sai na riska faɗinsa: "Babu wani musulmin da zai yi alwala ya kyautata alwalarsa, sannan ya tashi ya yi sallah raka'a biyu, yana mai fuskantarsu da zuciyarsa da fuskarsa, sai aljanna ta wajaba gareshi" Ya ce: Sai na ce: Ya mamakin kyan wannan, sai ga wani mai magana a gabana yana cewa: Wacce ke gabanta ta fi kyau, sai na duba sai ga Umar ya ce: Lallai ni na ganka ka zo ɗazu, ya ce: "Babu wani daga cikinku da zai yi alwala sai ya kai matuƙa - ko sai ya cika - alwalar sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah kuma (Annabi) Muhammadu bawanSa ne kuma ManzonSa ne sai an buɗe masa kofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so".
الترجمة
العربية বাংলা Bosanski English Español فارسی Français Bahasa Indonesia Русский Tagalog Türkçe اردو 中文 हिन्दी Tiếng Việt Kurdî Português සිංහල অসমীয়া Kiswahili ગુજરાતી Nederlands አማርኛ پښتو नेपाली ไทย മലയാളം Кыргызча Română Malagasy Svenskaالشرح
Annabi - tsira da amincin Alah su tabbata agare shi - ya yi bayani alhali shi yana zantar da mutane falala biyu masu girma: Na farko: Wanda ya yi alwala sai ya kyautata alwalar ya cikata ta fuskar da aka sunnanta, kuma ya ba kowace gaɓa haƙƙinta na ruwa, sannan ya ce: Ina shaida cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, kuma (Annabi) Muhammad bawan Allah ne kuma ManzonSa ne; sai an buɗe masa ƙofofin aljanna takwas zai shiga ta wacce yake so. Na biyu: Wanda ya yi wannan alwalar cikakkiya, sannan ya tashi bayan alwalar ya yi sallah raka'a biyu; yana mai fuskantosu da zuciyarsa da ikhlasi da ƙanƙar da kai, ya ƙanƙar dakai da fuskarsa da dukkan gaɓɓan jikinsa saboda Allah, sai aljanna ta wajaba gare shi.فوائد الحديث
Girman falalar Allah - Maɗaukakin sarki - ta hanyar ba shi lada mai girma akan ƙaramin aiki.
Shar’antuwar cika alwala, da yin sallah raka'a biyu da khushu'i a bayanta, da abinda ake samu na lada mai girma.
Cika alwala, da yin wannan zikirin a bayanta, yana daga sabubban shiga aljanna.
An so faɗin wannan zikirin ga mai wanka ma.
Kwaɗayin sahabbai akan alheri na neman ilimi da yaɗa shi, da taimakekeniyarsu akan hakan da kuma al'amuran rayuwarsu.
Zikiri bayan alwala a cikinsa akwai tsarkake zuciya da tsarkaketa daga shirka, kamar yadda cewa alwala a cikinta akwai tsarkake jiki da tsarkake shi daga datti.
التصنيفات
Sunnoni da Ladaban Al-wala