إعدادات العرض
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu
Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu
Daga Abdullahi ɗan Zaid - Allah Ya yarda da shi -: Lallai Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya yi alwala sau biyu-biyu.
[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]
الترجمة
العربية English မြန်မာ Svenska Čeština ગુજરાતી አማርኛ Yorùbá Nederlands اردو Bahasa Indonesia ئۇيغۇرچە বাংলা Türkçe සිංහල हिन्दी Tiếng Việt తెలుగు Kiswahili ไทย پښتو অসমীয়া دری Кыргызча Lietuvių Kinyarwanda नेपाली മലയാളം Bosanski Italiano ಕನ್ನಡ Kurdî Oromoo Română Soomaali Shqip Српски Українська Wolof Moore Tagalogالشرح
Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya kasance a wasu lokutansa idan zai yi alwala yana wanke Kowacce gaɓa daga gaɓɓan alwalarsa sau biyu, sai ya wanke fuska - daga cikin wankewar akwai kuskurar baki da shaƙa ruwa - da hannaye da ƙafafuwa sau biyu.فوائد الحديث
Wajibi a wanke gaɓɓan alwala (shi ne) sau ɗaya abin da ya ƙaru, to, shi mustahabbi ne.
Halaccin alwala sau bibiyu a wasu lokutan.
Abin shar'antawa a shafar kai (shi ne) sau ɗaya.