Kayi sallah a Qasa in zaka iya, idan kuma ka kasa to kayi nuni, kasanya Sujadarka Qasaqasa da ruku'unka.

Kayi sallah a Qasa in zaka iya, idan kuma ka kasa to kayi nuni, kasanya Sujadarka Qasaqasa da ruku'unka.

Daga Jabir Bn Abdullahi -Allah ya yarda da su- cewa Manzon ALlah SAW ya je duba mara lafiya sai ya ganshi yana sallah akan Matashi, sai ya xauke matashin yayi jifa da shi, sai ya xauki sanda don ya dogara da ita yayi sallah, sai ya kwace ya jefar da ita, kuma ya ce: "Kayi sallah a Qasa in zaka iya, idan kuma ka kasa to kayi nuni, kasanya Sujadarka Qasaqasa da ruku'unka"

[Ingantacce ne] [Bazzar ne Ya Rawaito shi]

الشرح

Wannan Hadisin mai girma yana bayanin yadda Mara lafiyar da ba zai iya kafa goshinsa a Qasa ba zai yi, kuma cewa wajibi ne akan Mai sallah gwargwadon ikonsa, kuma nuni a halin Ruku'u da sujada, kuma ya kasance Sujadarsa tafi qasaqasa daga Ruku'unsa

التصنيفات

Sallar Masu Uzuri