Haqiqa an tsorata ni a tafarkin Allah irin tsoratawar da ba'a yiwa kowa ba, kuma Haqiqa an cutar da ni irin cutarwar da ba'a yiwa kowa ba, Nayi kwana Talatin tsakanin Dare da Rana bani da Abincin abincin da zan ci ni da bilal sai Xan wani abu da zai kare cibiyar Bila

Daga Anas -Allah ya yarda da shi ya ce: Manzon Allah SAW ya ce: "Haqiqa an tsorata ni a tafarkin Allah irin tsoratawar da ba'a yiwa kowa ba, kuma Haqiqa an cutar da ni irin cutarwar da ba'a yiwa kowa ba, Nayi kwana Talatin tsakanin Dare da Rana bani da Abincin abincin da zan ci ni da bilal sai Xan wani abu da zai kare cibiyar Bila"

[Ingantacce ne] [Ibnu Majah ne ya Rawaito shi - Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah SAW ya faxa cewa a cewa shi kaxai ne a farkon bayyanar Addinin sai Kafirai suka bashi tsoro saboda hakan kuma suka cutar da shi, kuma babu wani tare da shi da zai kare masa cutarwar sai taimakon Allah da kariyarsa da kuma datarwarsa sannan yayi bayanin cewa duk da haka ga qarancin kuxi da Abinci da rashin tanadi, yadda zai kwana Talatin bashi da Abinci sai xan kaxan da Bilal zai iya voyeshi a qasan Hammatarsa, kuma ko tukunyar da zasu saka abincin babu, wannan shi ne lokacin da ya futa SAW yana mai guduwa daga Makka.

التصنيفات

Lokacin Makka