Kowane Manzo yana da mataimaka Mataimakina Al-zubair

Kowane Manzo yana da mataimaka Mataimakina Al-zubair

Daga jabir -Allah ya yarda da su- ya ce Manzon Allah SAW ya ce: "wa zai zo mun da Labarin Mutane ? a Ranar Yaqin ahzab, Zubair ya ce: Ni sannan ya ce: "Waye zai zo mun da labarin Mutane" Zubai ya ce: Ni Sai manzon Allah SAW ya ce: "Kowane Manzo yana da mataimaka Mataimakina Al-zubair"

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Yayin da ya kasance ana yaqin Ahzab sai Quraishawa suka zo da su da wasu zuwa Madina; don su yaqi Musulmai sai Manzon Allah ya haqa gwalalo labari ya jewa Musulmai cewa Bani Quraiza daga Yahudawa sun warware Alqawarinsu wanda sukai tare da Musulmai, sai Annabi SAW ya ce: "wa zai zo mun da Labarin Mutane ? a Ranar Yaqin ahzab, Zubair ya ce: Ni sannan ya ce: "Waye zai zo mun da labarin Mutane" Zubai ya ce: Ni Sai manzon Allah SAW ya ce: "Kowane Manzo yana da mataimaka Mataimakina Al-zubair"

التصنيفات

Falalar Sahabbai -Allah yayarda da su-