Annabi yayi Hajji tare da ni a Hajin bankwana, kuma ni ina Dan shekara Bakwai

Annabi yayi Hajji tare da ni a Hajin bankwana, kuma ni ina Dan shekara Bakwai

An karbo daga Al-Sa'ib Bn Yazid -Allah ya yarda da su- ya ce:Annabi yayi Hajji tare da ni a Hajin bankwana, kuma ni ina Dan shekara Bakwai

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Al-Sa'ib Bn Zaid -Allah ya yarda da su- Karamin Sahabi ne, Iyayensa sunyi Hajji da shi a lokacin Annabi ya riski Hajjin bankwana, kuma Annabi ya tabbatar da Hajjin Yara, kuma an kirga musu ita a Hajjin Tadawwu'i, sai dai yazama dole iodan ya Balaga yayi wani Hajjin don Sauke Farali, kuma Yaro zaiyi irin abunda Manya suke yi na Harama da rashin sanya dinkakkun kaya da yin Talbiyya da waninta, to idan ya kasa yi sai Waliyyinsa yayi masa, Kamar Babansa ko Mahaifiyarsa.

التصنيفات

Hukunce Hukunce da Ma'alolin Hajji da Umra