Manzon Allah ya hana sanya alhariri sai a gurin yatsu biyu, ko uku, ko hudu.

Manzon Allah ya hana sanya alhariri sai a gurin yatsu biyu, ko uku, ko hudu.

Daga Umar Dan Khaddab -Allah ya yarda da shi- cewa: Manzon Allah tsira da amincin Allah- " ya hana sanya Alhariri sai dai haka, sai ya daga mana yatsunsa biyu: Manuniya da y'ar tsakkiya". A wata ruwayar Muslim "ya Manzon Allah tsira da amincin Allah Manzon Allah ya hana sanya alhariri sai a gurin yatsu biyu, ko uku, ko hudu."

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Lallai Manzon Allah tsira da amincin Allah ya hana maza sanya alhariri sai dai a inda aka kebance, watau y'an yatsu biyu da aka ambata cikin hadisin Buhari da Muslim da ya gabata da kuma ruwayar Muslim da ta kara da cewa: ko uku ko hudu, don haka sai a yi amfani da mafi yawa, shi ne gwargwadon yatsu hudu ba laifi. ka duba Littafin Taasisil'Ahkam

التصنيفات

Ladaban Tufafi