Wata rana Na hau saman gidan Hafsa, sai Naga Annabi -tsira da aminci yana biyan bukatarsa, ya fuskanci Sham, ya juyawa Ka'aba baya.

Wata rana Na hau saman gidan Hafsa, sai Naga Annabi -tsira da aminci yana biyan bukatarsa, ya fuskanci Sham, ya juyawa Ka'aba baya.

Daga Abdullahi Dan Umar -Allah ya yarda dasu- yace: (Wata rana Na hau saman gidan Hafsa,sai naga Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- yana biyan bukatarsa ya fuskanci Sham,ya juyawa Ka'aba baya). A wata ruwayar((ya fuskanci Baitalmakdis)).

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Dan Umar -Allah ya yarda dasu- wata rana yazo gidan 'yar'uwarsa Hafsa,Matar Annabi -tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi-sai ya hau saman gidanta, sai ya gano Annabi -tsira da aminci su tabbata a gare shi- yana biyan bukatarsa ya fuskanci Sham,ya kuma juyawa Alkibla baya.Dan Umar Allah ya yarda da shi- ya fadi haka don yin raddi ga wadanda suka ce:Annabi baya fuskantar Baitalmakdis lokacin biyan bukata,daga nan kuma sai Mawallafin ya zo da ruwaya ta biyu wacce take cewa: yana mai fuskantar Baitalmakdis.

التصنيفات

Ladaban biyan bukata