Kada dayanku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi.

Kada dayanku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi.

An karbo daga Abu Huraira - Allah ya yarda da shi - an daga shi zuwa g Annabi: 'kar waninku ya yi fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, sannan ya yi wanka da shi" A wata ruwayar: 'kar waninku ya yi wanka da ruwan da ba ya gudan alhali yana da janaba"

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi mai tsira d a aminci ya yi hani ga yin fitsari a cikin ruwan da ba ya gudana, saboda hakan ka iya janyo cakuduwarsa da najasa da cututtukan da fitsarin ke dauke da su, wanda sa iya cutar da wanda ya yi amfani da su, ta iya yiwuwa mai yin fitsarinma da kanshi zai iya yin wanka da shi. to ta yaya zai yi fitsari cikin abin da zai iya zama abin tsarkinsa. Hakanan kuma ya yi hani ga yin wankan janaba a cikin ruwan da ba ya gudana; saboda yin hakan zai iya bata ruwan da datti da kazantar janaba.

التصنيفات

Hukunce Hukuncen Ruwa, Wanka