Na kasance ina wanke janaba daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- sai ya fita izuwa salla, koda ruwa yayi jirwaye a tufafin

Na kasance ina wanke janaba daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi- sai ya fita izuwa salla, koda ruwa yayi jirwaye a tufafin

Daga A`isha -Allah ya kara yarda a gareta- ta ce: ((Na kasance ina wanke janaba daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi sai ya sai ya fita izuwa masallaci, alhalin lallai akwai danshi a jikin tufafin nashi)). a cikin wata ruwayar kuma: ((Hakika na kasance ina kankare shi daga tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi kamkarewa, sai yayi sallah a cikin shi))An Hanamu bin raka Jana'iza amma kuma ba hanin dole ba

[Ingantacce ne] [Muslim ne ya rawaito shi - Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

A`isha Allah ya kara yarda da ita tana ambatar: cewa maniyyin janaba ya kasance yana shafar tufafin manzon Allah mai tsira da aminci su kara tabbata a gareshi, wani lokacin yana kasancewa danye sai ta wankeshi daga tufafin da ruwa, sai ya fita zuwa salla, alhalin ruwan bai gama bushewa daga tufafin ba, wani lokacin daban kuma, maniyyin yana kasancewa busashshe, a wannan lokacin sai ta kankare shi daga tufafin nashi kankarewa, sai yayi salla a cikinsa.

التصنيفات

Wanka