Duk wanda ya ciyar a tafarkin Allah za'a rubuta masa ninkin Lada sau dari bakwai.

Duk wanda ya ciyar a tafarkin Allah za'a rubuta masa ninkin Lada sau dari bakwai.

An rawaito daga Abu YahayaBin Khuzaim Bn Fatik -Allah ya yarda da shi- zuwa ga Annabi: "Duk wanda ya ciyar a tafarkin Allah za'a rubuta masa ninkin Lada sau dari bakwai."

[Ingantacce ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi - Al-Nasa'i Ya Rawaito shi - Ahmad ne ya rawaito shi]

الشرح

Duk wanda ya ciyar da kadan ko wani abu mai yawa a kan tafarkin Allah Madaukakin Sarki, walau na jihadi ne saboda Allah - Madaukaki - ko kuma a wasu bangarorin na adalci da biyayya, Allah zai ninka ladarsa a Ranar Kiyama har sau dari bakwai.

التصنيفات

Falalar Ayyuka na qwarai