"Boni ya tabbata ga wanda yake zantar da Mutane sai yayi Karya don Mutane suyi Dariya, Boni ya tabbata a gare shi sannan Boni ya tabbata a gare shi"

"Boni ya tabbata ga wanda yake zantar da Mutane sai yayi Karya don Mutane suyi Dariya, Boni ya tabbata a gare shi sannan Boni ya tabbata a gare shi"

An Rawaito daga Mu'awiya Bn Haidah -Allah ya yarda da shi ya ce Mazon Allah -tsira da Amincin Allah su tabbata a gare shi ya ce: "Boni ya tabbata ga wanda yake zantar da Mutane sai yayi Karya don Mutane suyi Dariya, Boni ya tabbata a gare shi sannan Boni ya tabbata a gare shi"

[Hasan ne] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Cikin wannan Hadisi akwai tsawatarwa mai tsananani daga Karya da kuma Narko ga wanda yake Karya saboda Raha da sanya Mutane dariya, saboda haka ya Zamanto mafi Munin Masu Muni, Kuma aka girmama Haramcinsa, to wannan yana daga cikin Munanan Halayan da suka Wajaba kan Mumini ya tsarkake Kansa daga su, Kuma ya nisanta daga su, kuma ya tsaekake Harshensa cikin kowane Hali daga cikin Halayan da ya samu kansa, sai abunda Shari'a ta yi masa Izini a cikinsa, Kamar yadda yake ya haramta yin zancen Karya saboda Raha kamar yadda ya haramta sauraron ta idan suka san cewa Karyar ce ya Wajaba akansu Inkarinta.

التصنيفات

Falaloli da Ladabai, Munanan Halaye, Ladaban Magana da kuma shiru