Falaloli da Ladabai

Falaloli da Ladabai

84- "Lallai cewa Allah zai tseratar da wani mutum daga al'ummata agaban halittu a ranar Alkiyama*, sai Ya bude masa fayil dinsa x asa'in da tara, kowanne fayil tamkar iya ganinka ne, sannan Ya ce: Shin kana musun wani abu daga wannan? Shin marubutaNa masu kiyayewa sun zalinceka ne? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai Ya ce: Shin kana da wani hanzari? Sai ya ce: A'a ya Ubangiji, sai (Ubangiji) Ya ce: Eh, lallai kanada wani abu kyakkyawa a wurinmu, a yau babu wani zalinci akanka, sai a fitar da wani kati a cikinsa akwai: Ina shaidawa cewa babu abin bautawa da gaskiya sai Allah , kuma ina shaidawa cewa Annabi Muhammad bawanSa ne kuma ManzonSa ne, sai ya ce: ka zo wajan ma'aninka, sai ya ce; ya Ubangiji wannan wanne katine tare da wadannan fayilillikan? Sai Ya ce; Lallai cewa kai ba za’a zalinceka ba, sai ya ce: Sai a dora fayilillikan a bangaren ma'auni , katin kuma a daya ma'aunin, sai fayililliakn su yi sauki, kuma katin ya yi nauyi, wani abu ba zai yi nauyi tare da sunan Allah ba".

85- "Yayin da Allah Ya halicci Aljanna da wuta, sai Ya aiki (Malaika) Jibril - aminci ya tabbata agare shi* - zuwa Aljanna, sai ya ce: ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta sai ya dawo, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa wani daya ba zai ji ta ba sai ya shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan ki, sai Ya ce; Tafi zuwa gareta ka yi duba zuwa gareta da kuma abinda na yi tanadi ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga ta an kewayeta da abubuwan ki, sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa shiga cikinta . Ya ce: Tafi ka yi duba zuwaga wuta da kuma abinda na tanada ga ma'abotanta a cikinta. Sai ya yi duba zuwa gareta, sai ga shashininta yana hawa kan sashi, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa ba wanda zai shigeta. Sai ya yi umarni da ita sai aka kewayeta da abubuwan sha'awa , sai ya ce; ka koma ka yi duba zuwa gareta, sai ya yi duba zuwa gareta sai ga shi ita kuma an kewayeta da abubuwan sha’awa, sai ya dawo sai ya ce: Na rantse da buwayarKa hakika na ji tsoron kada wani daya ya kasa tsira daga gareta a ce bai shigeta".