((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa

Daga Abu Huraira - Allah Ya yarda da shi - daga Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: ((Ku nisanci abubuwa bakwai masu halakarwa)) suka ce: Ya Manzon Allah, wadanne ne su? Ya ce: “Shirka da Allah, da sihiri, da kashe rai wacce Allah Ya haramta sai da gaskiya, da cin riba, da cin dukiyar maraya, da juya baya ranar yaki, da yiwa mumina katangaggiya rafkananniya kazafi".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - yana umartar al'ummarsa da nisantar laifuka da sabo guda bakwai masu halakarwa, yayin da aka tambaye shi game da su wadanne ne su? sai ya bayyana su da cewa su ne: Na farko: Shirka da Allah, ta hanyar rikon kishiya da tamka gare Shi - tsarki ya tabbatar maSa - daga dukkanin wani zance da ya kasance, da kuma juyar da kowace irin ibada daga ibadu ga wanin Allah - Madaukakin sarki - kuma ya fara da shirka; domin cewa ita ce mafi girman zunubai. Na biyu: Sihiri - shi ne wani na daga kullace-kullace da wasu magunguna da hayake-hayake -, yanayin tasiri a cikin jikin wanda aka yi wa sihirin ta hanyar kisa ko rashin lafiya, ko ya raba tsakanin ma'aurata biyu, shi aiki ne na Shaidan, kuma da yawa daga gare shi ba'a kaiwa zuwa gareshi sai ta hanyar shirka da neman kusanci zuwa ga munanan ayyuka da wani abin da suke so. Na uku: Kashe ran da Allah Ya hana kashe ta ba da wani abinda ya halatta a shari'ance wanda shugaba zai zartar dashi. Na hudu: Amfani da riba ta hanyar ci ko waninsa ta fuskokin amfani. Na biyar: Barna akan dukiyar karamin yaron da babansa ya mutu alhali shi bai kai shekarun balaga ba. Na shida: Guduwa daga yaki da ake yi da kafirai. Na bakwai: Tuhumar 'ya'ya mata kamammu da zina, haka nan ma tuhumar maza.

فوائد الحديث

Lallai cewa manyan zunubai ba su takaitaba a guda bakwai ba, kuma kebance wadannan bakwan dan girmansu ne da kuma hadarinsu.

Halaccin kashe rai idan ya kasance da hakki ne kamar kisasi da ridda da zina bayan katangantuwa, kuma shugaba na shari'a shi ne yake zartar da shi.

التصنيفات

Munanan Halaye, Zargin Savo