Kunya tana daga imani

Kunya tana daga imani

Daga Abdullahi ɗan Umar - Allah Ya yarda da su - ya ce: Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi - ya ji wani mutum yana yi wa ɗan uwansa wa'azi game da kunya, sai ya ce: "Kunya tana daga imani".

[Ingantacce ne] [Bukhari da Muslim suka Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ji wani mutum yana yi wa wani ɗan uwansa nasihar cewa ya bar yawan kunya! sai ya bayyana masa cewa kunya tana daga imani, kuma ba ta zuwa sai da alheri. Kunya ɗabi'a ce da take sa aikata mai kyau da barin mummuna.

فوائد الحديث

Abin da zai hana ka alheri ba a ambatonsa kunya, kai ana ambatonsa tsoro da gajiyawa da rauni da ragonta.

Kunyar Allah - Mai girma da daukaka - tana kasancewa ne da aikata abubuwan da aka umarta, da barin abubuwan da aka hana.

Kunyar ababen halitta tana kasancewa ne da girmamasu, da saukar da su masaukansu, da nisantar abin da zai munana a al'adance.

التصنيفات

Kyawawan Halaye