إعدادات العرض
Kyawawan Halaye
Kyawawan Halaye
1- Idan mutum ya so dan'uwansa to ya sanar da shi cewa shi yana sonsa
5- Lallai Allah Ya wajabta kyautayi a kan kowane abu
8- Wanda aka haramtawa sauƙi to an haramta masa alheri
9- Kada ka wulaƙanta komai daga wani aikin alheri, ko da ka gamu da ɗan uwanka ne da sakakkiyar fuska
10- Mai ƙarfi ba shi ne gwanin kaye ba, kadai mai ƙarfi shi ne wanda yake mallakar kansa a yayin fushi
11- Wanda ya shiryar a kan wani alheri, to, shi ma yana da kwatankwacin ladan wanda ya aikatashi
12- Wanda ya kasance ya yi imani da Allah da ranar lahira, to, ya faɗi alheri ko ya yi shiru
13- Wanda ba ya jin ƙan mutane Allah - Mai girma da ɗaukaka - ba zai ji ƙansa ba
17- Wanda ya kare mutuncin ɗan uwansa Allah Zai kare fuskarsa daga wuta a ranar al-ƙiyama
18- Lalle Allah Yana son bawa mai tsoronSa, wanda ya wadatu, mai ɓoye kansa
21- Lalle mumini yana riska da kyawawan dabi’unsa matsayin mai azumi da mai tsayuwar dare
22- Lalle masu kyawawan dabi’unku suna cikin zaɓaɓɓunku
23- Ku sauƙaƙa kada ku tsananta, ku yi bushara kada ku yi kora
24- Masu jin ƙai (Ubangiji) Al-Rahman yana jin ƙansu, ku ji ƙan mutanen ƙasa wanda ke sama zai ji ƙanku
25- Wani bawa ba zai suturta wani bawa a duniya ba sai Allah Ya suturta shi a ranar Alƙiyama
28- Ɗayanku ba zai yi imani ba, har sai ya sowa ɗan uwansa abinda yake sowa kansa
34- Mumini ba mai yawan suka bane ko mai yawan tsinuwa ba ko mai yawan alfasha ba ko mai zancen banza ba
