Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace

Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace

Daga Abu Musa al-Ash'ari - Allah Ya yarda da shi - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi - ya ce: «Ku ciyar da mayunwaci, ku duba mara lafiya, ku fanso wanda aka ribace».

[Ingantacce ne] [Buhari ne ya rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya bayyana cewa daga cikin haƙƙin musulmi akan ɗan uwansa musulmi shi ne ya ciyar da mayunwaci, ya ziyarci mara lafiya, ya fanso wanda aka ribace.

فوائد الحديث

Kwaɗaitarwa akan taimakekeniya tsakanin musulmai.

Kwaɗaitarwa akan ciyar da mayunwaci mai buƙatar cin abinci, to wannan an yi umarni a ciyar da shi.

Halaccin gaida mara lafiya; dan rage masa raɗaɗi, da yi masa addu'a, da samun lada, da wanin haka.

Kwaɗaitarwa akan fansar wanda aka ribace idan kafirai sun ribace shi, hakan ko dai bada biyan wani abuba dan tsamo shi daga cikinsu, ko ta hanyar musayar fursuna kafiri daga cikin waɗanda aka ribato; wato: Ta hanyar musaya.

التصنيفات

Kyawawan Halaye