Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u

Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u

Daga Abu Zarr, Jundubu Ibnu Junadata, da Abu Abdurrahman, Mu'azu Ibnu Jabal - Allah Ya yarda da su - daga Manzon Allah - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya ce: «Ka ji tsoron Allah a duk inda kake, kuma ka bi munanan (ayyuka) da kyakkyawa zai shafe shi, ka ɗabi'anci mutane da kyawawan ɗabi'u».

[قال الترمذي: حديث حسن] [Al-Tirmithi Ya Rawaito shi]

الشرح

Annabi - tsira da amincin Allah su tabbata agare shi - ya yi umarni da al'anura uku: Na farko: Tsoron Allah hakan ta hanyar aikata wajibai, da barin abubuwan da aka haramta, a kowane guri da zamani da kuma hali, a ɓoye da bayyane, haka a lokacin lafiya da bala'i da wanin haka. Na biyu: Idan ka afka cikin mummunan (laifi), to ka aikata kyakkawan (aiki) a bayan shi, kamar sallah da azimi da sadaka da aikin alheri da sada zumunci da wanin haka, domin cewa hakan zai shafe mummuna. Na uku: Ka yi wa mutane mu'amala da kyawawan ɗabi'u, na murmushi a fuskokinsu, da tausasawa da aikata alheri da kamewa daga cutarwa.

فوائد الحديث

Falalar Allah - Mai girma da ɗaukaka - ga bayi a kan rahamarSa da gafararSa da kuma rangwaminSa.

Hadisin ya ƙunshi haƙƙoƙi uku: Haƙƙin Allah da taƙawa, da haƙƙin rai ta hanyar aikata kyawawan halaye bayan munanan (halaye), da kuma haƙƙin mu'amala ta hanyar aikata kyawawan ɗabi'u.

Kwaɗaitarwa akan aikata kyawawan (halaye) bayan munanan (halaye), da kyawawan ɗabi'u, na ɗabi'un tsoron Allah, kawai an ambace su da ambato ne dan buƙatuwa zuwa ga bayaninsu.

التصنيفات

Kyawawan Halaye